Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hakokin Ma'aikatan Kamfanin Lantarki Sun Makale a Hannun Gwamnatin Tarayya


Shugaba Goodluck Jonathan wanda gwamnatinsa ta sayarda kamfanin lantarki ko PHCN

Biyo bayan sayarda kamfanin lantarki na Najeriya ko PHCN gwamnatin tarayya ta dauki biyan ma'akatan da ta sallama to amma tun 2013 da tayi hakan har yanzu bata gama biyansu ba

Tun a cikin watan Nuwamban shekarar 2013 ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta sallami ma'akatan kamfanin lantarki ko PHCN saboda sayarda kamfanin ga 'yan kasuwa.

Sallamar ta shafi ma'akata fiye da dubu hudu. Biyan hakokinsu kuma ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayyar Najeriya. Kawo yanzu dai an biya kimanin kashi sittin cikin dari na ma'aikatan. Amma har yanzu sauran kashi arba'in din na cigaba da bibiyar lamarin.

Malam Jibrilu Muhammad kakakin ma'akatan da aka sallama a shiyar Kano wadda ta kunshi jihohin Kano da Jigawa da Katsina yace akwai ma'akata fiye da dubu guda a shiyar dake cikin halin kunci sanadiyar makalewar hakokinsu a hannun gwamnati..

Malam Muhammad yace gwamnati ce tayi masu alkawarin biyansu hakokinsu yayinda ta sayar da kamfanin PHCN. Yace an biya wasu amma su ba'a biyasu ba. Wasu daga cikinsu sun sha jira har ma sun rasu. Wani ma barayi sun bishi har gida suka tambayeshi kudin da aka biyashi yace babu aka kuma kasheshi. Malam Muhammad ya roki gwamnatin shugaba Jonathan da ta biyasu kafin ta sauka.

Banda wadanda suka mutu ko suka kamu da rashin lafiya akwai wadanda ke cikin halin ni-iyasu a halin yanzu. Wani Nura Garba yace wata tara ba'a biyashi ko kwandala ba. Diyarsa ba karatu domin babu abun da zai biya kudin makarantarta da shi. Shi ma Bala Garba yace tun ranar da aka sallamesu babu abun da ya shiga hannunsa.'Yanuwa da abokan arziki suke taimaka masa. Yana da mata biyu da 'ya'ya goma sha daya.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG