Accessibility links

Har Yanzu Babu Wanda ya Nemi a Raba Najeriya-Indabawa

  • Aliyu Imam

Gungun 'yan Najeriya a wata zanga zanga da suka gudanar a Abuja.

Kwamitin jin ra'ayoyin jama'a kan taron kasa yana jihar kaduna, kuma yace har yanzu babu wanda yake neman a rabakasar.

Kwamitin da shugaban Najeriya ya kafa domin tattara bayanai da ra’ayoyin ‘yan kasa dangane da taron kasa, ya isa jihar Kaduna, kuma ana sa ran kwamitin ya kammala zaman sauraron shawarwari daga wannan shiyyar a talatan nan.

Da yake magana da wakilinmu a yankin sakataren kwamitin Dr. Akilu Sani Indabawa, yace alamar nasarar aikinsu shine ganin cewa har yanzu babu mutum ko wata kungiya da ta fito ta bada shawarar a raba Najeriya. Dr. Indabawa ya kara da cewa babban abunda kwamitin yake bukata shine hadin kai, kuma ko wani dan Najeriya ya fahimci cewa yana da ‘yancin fadin ra’ayinsa, su kuma aikinsu ne su saurari wannan ra’ayi, su rubuta su mikawa gwamnati cikin rahoton aikin da aka basu.

Amma jigon wata kungiyar rajin kare muradun arewa mai suna “Arewa Defense League” da turanci, Mallam Murtala Abubakar, yace kungiyarsa tana mai ra’ayin a raba kasar domin acewarsa,ahalin yanzu ana cutan ‘yan arewa, inda ‘yan yankin Niger Delta suke matsayin ‘yan mowa, saura kuma ‘yan bora. Yace a tsarin zaman tarayya, ana zaman ka taimakeni ne ni kuma in taimaka maka.

Ana sa gudumawar, sakataren kungiyar muriyar talakawa komorade Bishir Dauda, yace kuskure ne ga ‘yan arewa idan suka kauracewa wannan taron. Kauaracewa taron yace zai nuna kamar arewa tana tsoron zaman. Na biyu kuma, taron zai baiwa ‘yan arewa damar gabatar da bukatunsu, da irin gudumawa da suke bayarwa a fannin raya tattalin arzikin kasa. Bishir yace, alal misali arzikin kasa da ake magana akai kamar man fetur akwai wanda ake haka a doron kasa da kuma a can cikin teku, yace yadda ake raba wannan arziki ba a yinsa dai dai.

Cikin tawagar jihar katsina har da mai shari’a Mamman Nasir mai ritaya, wanda shi ma ya gabatar da kasida. Mai shari’a Nasir, yace wannan taro ba ta siyasa bace, kuma idan aka gudanar da ita ba tareda wani son zuciya ba, to za a sami fa’ida.

Tawagar jihar Kano ta nemi janyo hatsayina a zaman taron jiya litinin, domin kamar yadda take cewa, babu ma bukatar a yi wannan taro.

Kwamitin zai saurari ra’ayoyi daga jihohin Jigawa, da kano, da Katsina, da mai masaukin baki jihar kaduna.
Ga rahoton wakilinmu Isa Lawal Ikara.

XS
SM
MD
LG