Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Yemen Bai Yi Nasara Ba - White House


Shugaban Amurka Donald Trump

Mai Magana da yawun gwamnatin Donald Trump ya fada cewa samamen da Amurka ta kaiwa kungiyar al’Qaida a Yemen ranar Lahadi ba za a ce an yi nasara ba, idan aka yi la’akkari da mutane sama da 12 da suka mutu, ciki ko har da farar hula da kuma soja. Amurka guda.

Sean Spicer ya fada wa manema labarai jiya Alhamis cewa samamen abu ne da aka tsara shi sosai wanda kuma shugaba ya ba da umurnin a gudanar dashi tun a ranar 26 ga watan jiya.

Sai dai Spicer ya ce an fara tunanin kai wannan harin ne tun a ranar 7 ga watan Nuwamba, ranar jajiberen zaben shugaban kasar Amurka, lokacin da Barack Obama ne shugaban kasa.

Spicer ya jaddada cewa ba shakka an tsara wannan samamen kwarai da gaske kafin a aiwatar da shi.

Haka kuma duk a jiyan ne cibiyar kula da yake-yaken da Amurka ta ke yi, ta ce tana binciken wannan samamen, kuma ta tabbatar da cewa farar hula ciki har da yara suna cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Mai Magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Pentagon ya ce ba mamaki harbi daga jirgin yakin Amurka ne ya kashe farar hulan.

Shi ma a jiya mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Jeff Davies, ya tabbatar cewa mata na cikin jerin zaratan sojojin da suka kai wannan samamen.

XS
SM
MD
LG