Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harkokin Tsaro Na Ci Gaba Da Tabarbarewa A Kasar Kamaru


Shugaban Kamaru, Paul Biya
Shugaban Kamaru, Paul Biya

Duk da jibge dimbin jami’an tsaro a jihohi biyun dake tawaye inda ake anfani da harshen Turanci, har yanzu harkokin tsaro sai ci gaba da tabarbarewa su keyi

Matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a jihohin ’yan aware guda biyu wadanda suke amfani da harshen turanci.

Duk da cewa gwamnatin Kamaru ta cika jihohin da jami’an tsaro amma har yanzu, ta kasa shawo kan lamarin.

Alhaji Abdulkadiri mazaunin Birnin Baminga yace lamarin tsaro na kara ta’azzara saboda abinda Kudancin Kamaru ke yi. Ya ce an kama mutane an kulle su. An kamo shugaban su daga Nigeria shima, an tsare shi. An kona gidajensu, kuma gwamnati bata dauki matakan kawo zaman lafiya ba.

Alhaji Abubakar wanda yake cikin kwamitin da gwamnatin Kamaru ta kafa domin wanzar da zaman lafiya a bangaren ‘yan awaren ya ce abun da gwamnati ta tsara domin taimakawa ‘yan tawayen yana da mahimmanci. Akan cewa gwamnati ta tausaya masu akan irin hasarar da suka yi. Ita ma gwamnatin ta yi hasarar makarantu. Ministan harkokin cikin gida yace, gwamnati zata bada umarnin soma aikin gyara wuraren da aka lalata harda makarantu.

Musa Useni dan kungiyar kare hakkin bil Adama a Kamaru ya ce matakan da suke dauka su ne ta hanyar tuntubar gwamnati da fahimtar dasu domin su shawo kan ‘yan tawayen zuwa teburin yin shawarwari inda zasu samu su tattauna hanyoyin samun masalaha. Abu na biyu kuma yaran da gwamnati ta kwashe da ba’a san inda suke ba za’a fadakar da gwamnati illar dake tattare da ci gaba da yin hakan.

A saurari rahoton Muhammad Awal Garba

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG