Accessibility links

Helkwafta Ta Sojan Sham Ta Fadi A Damascus


Hayaki na tashi sama a tsakiyar gari yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a kasar Sham

Gidan telebijin na Sham yace jirgin sojan ya fado a Damascus ba tare da karin bayani ba, amma wasu rahotanni sun ce 'yan tawaye suka harbo shi

Wani helkwafta na sojan kasar Sham, ko Syria, ya fado a Damascus, babban birnin kasar, yayin da ake samun rahotannin ci gaban kazamin fada a tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a yankin.

Gidan telebijin na Sham ya bayar da rahoto litinin din nan cewa wani jirginb saman soja samfurin helkwafta ya fadi a Damascus, amma bai yi karin haske ba.

Wasu rahotanni sun ce 'yan tawaye ne suka harbo jirgin, wanda ya kama da wuta kafin ya subuto kasa. Wani hoton bidiyon da ba kwararren mai aikin hoto ya dauka ba, ya nuna wani jirgi yana ci da wuta bal-bal yana fadowa kasa.

Kungiyar kare hakkin bil Adama a kasar Sham mai hedkwata a kasar Britaniya, ta ce wannan jirgin helkwafta ya fado a wata unguwa mai suna Jobar a birnin na Damascus.
XS
SM
MD
LG