Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Jihar Neja Za Ta Hukumta Duk Wanda Ya Damfari Maniyatta


GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello

Hukumar alhazan jihar Neja tana daukan matakan ba sani ba sabo ga duk wanda aka samu yana damfarar maniyattan aikin hajji da sunanta.

A can baya an samu dimbin jama'a da suka yi asarar miliyoyin Naira da sunan za'a kaisu kasa Mai Tsarki, wato Saudiya domin sauke farali.

Biyo bayan abun da wasu jami'an hukumar alhazan jihar suka yi shekarar da ta gabata ya sa mutane suna tsoron yadda da hukumar akan ayyukan hajjin bana.

Shugaban hukumar alhazan na yanzu Adamu Idris Jabbi yace sun dauki matakin tabbatar da magance matsalar.Shugaban yana magana ne yayinda yake rabawa alhzan da suka yi aikin hajji a shekarar 2015 Naira miliyan 25, kudin da hukumar alhazai ta kasa ta mayar masu. Yace sun tsara biyan alhazan ta yadda kowa zai samu nashi.

Shugabannin kananan hukumomin jihar ne aka baiwa kudaden domin rabawa alhazansu na shekarar 2015 da yawansu ya kai dubu uku da dari biyu da goma sha biyu.

Shugaban karamar hukumar Mariga Abdulmalik Sarkin Daji yace wannan cigaba ne aka samu ga gwamnanti mai ci yanzu saboda ba'a taba samun irin haka ba, a ce bayan an kammala aikin hajji da wasu shekaru a dawo a ce kudade sun ragu a mayarwa alhazan. Yace wannan ya nuna adalci.

Shi ma Ado Abubakar shugaban karamar hukumar Tapa yace sun dauki abun da aka yi da farin ciki kuma alama ce ta samun canji a karkashin shugabancin Muhammad Buhari. Yayi alkawarin kirawo wadanda suke da kudaden su raba masu.

Abdulmalik Sarkin Daji yace matakan da aka dauka a wannan karon wajen biyan kujerun hajji zasu yi maganin cuwa-cuwa.

Ka rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG