Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Nijar Ta Dage Tashin Alhazai da Za'a Fara Yau Talata


Aikin Hajji

Sanadiyar rashin isar kudin alhazan Nijar kasa mai tsari ya sa hukumar alhazan kasar dage tashin alhazanta da ta shirya zata fara yi yau Litinin har zuwa wani lokaci nan gaba bayan da kudaden suka isa Saudiya

Yau 8 ga watan Agusta ya kamata ayarin farko na maniyattan Nijar ya tashi daga Yamai zuwa kasa mai tsarki domin soma ayyukan hajjin bana.

Amma a wata ganawa da shugabannin kamfanonin jiragen saman jigilar alhazan shugaban hukumar alhazai Alhaji Jibirin Labukari ya bayyana cewa tashin ba zai samu ba yau sakamakon wasu lallurori.

Inji shugaban hukumar alhazan kudaden da zasu yi anfani dasu basu isa asusun bankinsu ba a can kasar Saudiya. Sai kuma sun fara samun matasala wajen yiwa alhazan biza, wato takardar izinin shiga kasar ta Saudiya. Baicin hakan basu samu alhazai 560 da zasu cika jirgin farkon ba. Yakamata magungunansu a ce sun tafi a jirgin farko amma basu hadu ba.

Alhaji Labukari ya cigaba da cewa akwai matsala da gidajen da alhazan zasu sauka a Medina. Masu shirya masu gidajen basu gama ba tukunna. Wadannan dalilan suka sa suka dage tashin farko.

Sai dai hukumar tace akwai yiwuwar daidaita lamura ba tare da bata lokaci ba saboda ana kyautata zaton kudaden zasu shiga asusun hukumar gobe.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG