Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Hisbar Kano ta Tilastawa Wata 'Yar Wasan Kwaikwayo ta Bar Unguwar da Take


Sanusi Lamido Sanusi II, Maimartaba Sarkin Kano.

Biyo bayan korafe-korafen al'ummar unguwar Maidile dake Kano kan 'yan wasan kwaikwayo, hukumar hisba ta tilastawa wata 'yar wasan kwaikwayo dake hayan gida a unguguwar ta tashi

Matasa a unguwar Maidile dake Kano sun nuna rashin amincewar su da kasancewar wata ‘yar wasan kwaikwayo a unguwar, domin tana tara mata da maza a gidanta har su kai dare suna wasansu na kwaikwayo.

Sabili da yadda 'yar wasan kwaikwayon ke kawo mata da maza cikin dare ya sa al'ummar unguwar suka mika ukansu ga mai unguwa inda suka yi zargin tana hanasu barci kuma tamkar tana zubar da darajarsu ne. Ma ya nemi wadanda suka bata haya da sauran 'yan wasan nata su tadasu.

A kokarin kawo zaman lafiya mai unguwar da matasan unguwar da sun samu damar kama wasu daga ciki mazajen sun kuma mika su ga ‘yan Hisba. Abun da mai unguwar yayi ya sa daya daga cikin 'yan matan ta yiwa rayuwar mai unguwar barazana da wuka kana ta tafi caji ofis din 'yansandan unguwar inda ta shigar da nata koken. Su kuma 'yansandan sai suka kama mai unguwar domin yin bayani.

Shi mai unguwan, Malam Idris yace tabbas wannan lamari ya faru amma babban abun takaici shine ita wannan mata ta sa ‘yan sanda sun kama shi har an sa shi a bayan kanta.

Hukumar Hisba tace ta ummarci wannan mata bayan da aka samu mashala da ta bar unguwar domin rashin amincewar al'ummar unguwar da irin rayuwarta da sana'ar da ta keyi.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG