Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Tace Shan Barasa na Hallaka Mutane


Kwalaben giya

A wani rahoto da ta fitar hukumar kiwon lafiya ta duniya ta kiyasta cewa mutane fiye da miliyan uku shan barasa ke kashewa a duk fadin duniya kowace shekara.

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya ta tabbatar da cewa mutane miliyan uku da dubu dari uku suka mutu a shekarar 2012 sabili da shan barasa.

Rahoton ya nuna cewa akwai bukatar gwamnatoci su tashi tsaye domin su takaita zukar barasan tsakanin jama'a ta yadda za'a saukaka yaduwar cututukan da shan barasa ke haddasawa.

Haruna Aliyu mai aikin magunguna kuma mukaddashin babban sakatare na ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Neja yace shan barasa nada illoli da yawa. Na farko idan mutum ya sha barasa abubuwan da zata sa mutum yayi ba wadanda mai hankali zai so yayi ba ne. Idan ta huda mutum tana shiga cikin hantar mutum ta batata. Shan barasa kuma ya kan kawo tabin hankali. Barasa kuma tana bata wasu abubuwa cikin jikin mutum har ta kaiga mutuwa.

Alhaji Abdullahi Abdul kwamandan hukumar dake yaki da fataucin miyagun kwayoyi yace barasa na cikin kwayoyin da suke sa ido akai domin a tabbatar cewa an fadakar da mutane akan shanta. Shan giya ka iya sa mutum yayi wasu laifuka da zasu sa a daureshi.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG