Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Zata Takaita Fasa Kwabri Domin Kare Manufofin Noma


Shugaban hukumar kwastam na Najeriya, kanar Abdulhamid Ibrahim Ali, ya bayyana cewa nan da watanni uku masu zuwa hukumar zata matukar takaita fasa kwabri domin kare manufofin noma a Najeriya.

Shugaban hukumar kwastam ta kasa ya bayyana cewa hakkin su ne su tabbatar cewa manoma sun amfana daga shirye shirye da tsare tsaren gwamnati kan harkokin noma.

Wadannan maufofi batu ne na noman shinkafa hakazalika shima fasa kwabrin duk akan harkokin shinkafa ne. Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mayar da hankali sosai a kan noman shinkafa domin yanzu haka babban bankin Najeriya, na shirye shiryen taimakawa manoma shinkafa kimanin miliyan goma sha biyu.

Malam Shu’aibu Mungadi, mai sharhi ne kan al’amurran yau da kullum ya bayyana cewa babban kuskure ne idan gwamnati ta mayar da hankali wajan habaka noman shinkafa kadai, domin kuwa a cewar sa, kowane bangare na kasar nada irin amfanin da suke nomawa, dan haka wajibi ne a tallafawa dukkan nau’ukan noma, ban a shinkafa kadai ba.

Kwararre kan harkokin noma Alhaji Musa Ibrahim, kuma ya bayyana cewa a ganinsa dalilin da yasa gwamnati ta mayar da hankali kan noman shinkafa shine domin ita ce mafi akasarin amfanin gonar da ake shigowa da ita daga kasashen ketare.

Ya kuma kara da cewa idan gwamnati zata fadada noman zuwa gas u alkama, waken suya da noman rogo tund ana flawa da staci da shi, da sauran abubuwa daban daban daban da kuma samar da kananan masana’antu domin sarrafa kayayyakin goma, ta haka ne kawai hakarta zata cimma ruwa.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG