Accessibility links

Hukumar Kwastan ta Duniya ta Ziyarci Shugaban Najeriya


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Hukumar kwastan ta duniya ta kawo ziyara Najeriya ta ga yadda ake cigaba da ayyukan da aka karbe daga 'yan kwanjilar kasashen waje

A daidai lokacin da a ke takun saka tsakanin ma'aikatar kudi da hukumar kwastan din Najeriya domin yadda ake gudanar da ayyukan kwastan babban sakatare na hukumar kwastan ta duniya da tawagarsa ya kawo ziyara.

Babban sakataren na kwastan din duniya ya jagoranci tawagarsa ne domin ganawa da shugaban kasar Najeriya a kan hanyoyin da ya kamata a bi domin a inganta ayyukan kwastan. Na biyu tawagar tana son ta tabbatar cewa nasarorin da aka samu lokacin da gwamnatin tarayya ta sallami 'yan kwangila daga kasashen waje da suka yiwa hukumar kwastan ta Najeriya ayyuka na sama da shekara talatin an samu nasara da cin moriyarsa.

Bayan tawagar ta tattauna da shugaban kasa wakilin Muryar Amurka ya tuntubi shugaban hukumar kwastan ta Najeriya Alhaji Abdullahi Dikko Nde domin samun karin bayani kan mahimmancin ganawar.

Alhaji Nde yace yau wata na uku ke nan da suka karbi aiki daga 'yan kwangilar kasashen waje. Tawagar ta zo ne ta duba irin yadda Najeriya ke cigaba da ayyukan kwastan ba tare da wasu daga kasashen waje ba. Da babban sakatern ya sauka a Legas ya yiwa jam'an kwastan tambayoyi da ma 'yan kasuwa domin tabbatar da gaskiya. Shi da bakinsa yace bai taba ganin inda mutane suka hada kansu suna kishin kasarsu ba kamar yadda ya gani a Najeriya. Ya ga mutane da suke alfahari da farin cikin cewa yanzu 'yan Najeriya ne ke ayyukan da 'yan kasashen waje suka kwashe shekara talatin suna yi.

Ga rahoto da cikakken bayani.
XS
SM
MD
LG