Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IMF: Daga Watan Oktoban Badi Takardar Kudin China ta Shiga Jerin Kudaden Duniya


Christine Lagarde shugabar Asusun Bada Lamuni na Duniya ko IMF

Asusun bada lamuni na duniya ko IMF ya amince ya saka takardar kudin China cikin jerin kudaden duniya na musaya da kasuwanci a duk fadin duniya kamar dalar Amurka da sauransu

Asusun bada lamuni na duniya wato IMF, ya sanya takadar kudin China da ake kira Yuan cikin jerin kudade da zaiyi amfani da su. Hakan yana kunshe ne cikin sanarwa da bayanai da asusun ya bayar jiya Litinin.Ana ganin wannan mataki zai karawa kasar ta Sin kima ko daraja, China ce kasa ta biyu a girman tattalin arziki a duniya bayan Amurka.

Asusun IMF yace takardun kudi na Yuan wanda kuma ake kira Renminbi, "ya cika dukkan sharudda," saboda haka za'a shigar da shi kari kan kudaden Dalar Amurka, da takardun kudin Euro, da Yen na Japan, da pam na Ingila, a jerin kudade da asusun yake amfani da su. Mizani da IMF yake amfani da shi wajen bada rance ko lamuni ga kasashe 188 dake zaman wakilai a asusun. Matakin zai fara aiki ne daga watan Oktoba na badi.

Babbar darektar asusun Christine Legarde, tace yanke wannan shawara yana da muhimmanci a yunkurin shigar da tattalin arzikin China a jeri kudin duniya.

XS
SM
MD
LG