Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwambe Ta Biya Diyya Naira Milyan 230 Ga Mutane Samada 460 Don Aikin Hanyoyi.


Gwamna Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo.

Shugaban kwamitin biyan diyyar Alhaji Shehu Durbi ne ya bayyana haka a hira da Sashen Hausa na Muriyar Amurka.

Gwamnatin jahar Gwambe zata gina sabbin hanyoyi 7 cikin fadar jahar. Wannan aiki zai taba gidaje da wuraren ayyukan mazauna fadar jahar.

Domin haka ne gwamnatin ta kafa kwamiti da zai kula da biyan diyya karkashin jagorancin Alahji Shehu Durbi, wanda ya gayawa Abdulwahab Mohammed, cewa bayan kwanaki uku kwamitin ya biya kashi 95 cikin dari na diyyar.

Kwamitin ya biya mutane 468 Naira Milyan 229.6, domin yadda ayyukan gina wadannan hanyoyi zata shafi ko gidajensu ko wuraren ayyukansu.

Wadansu daga cikin wadanda aikin zai shafi gidajensu suna korafin cewa diyyar da aka biya su tayi kadan. Wadansu kuma suna yaba abunda aka basu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG