Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan Amurka a Najeriya Ya Yi Karin Haske Kan Dokar Trump


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson

Dokar hana mutane daga wasu kasashe bakwai inda musulmi suka fi rinjaye shiga Amurka ta kawo cecekuce da rudani a cikin Amurka kanta ta sauran kasashen duniya

Ganin yadda dokar ta shugaban Amurka Donald Trump ta kawo rudani da tashin hankalin jama'a ya sa Jakadan Amurka a Najeriya ya kira taron manema labarai domin ya yi masu bayani akan manufar dokar.

Jakadan yace sabon shugaban Amurka yana son ya tabbatar da ana da wani tsari mai inganci don baiwa mutanen dake son zuwa Amurka su zama wani bangare na amurkawa. Masu kuma bukatar ziyara ko karatu suna iya zuwa. Amma kuma kasar na son hana duk wadanda ka iya yi mata barazana shiga. Kowace kasa tana son ta tabbatar ana girmama dokokinta da kuma bin tsarinta.

Jakadan yace Amurka bata rufe kofofinta ga 'yan gudun hijira ba amma tana son daukan matakan rigakafi ne dangane da batun tsaro.

Da yake magana akan manufofin Donald Trump Jakadan yace manufar ita ce samun tsarin da zai yi aiki, wato duk wanda zai shiga Amurka a bi digdiginsa a san rayuwarsa da abun da ya keyi a kuma san abun da zai yi a Amurka. Amurka zata tabbatar mutanen kirki ne ke zuwa kasar ko menen jinsinsu ko addini.

Yanzu dai wata kotu ta jawa shugaban kasar Amurkan birki kuma gwamnatinsa ta daukaka kara. To ko menene zai biyo baya, Dr Kabiru Danladi Lawanti na Jami'ar Ahmadu Bello yace idan bai ci nasara ba a kotu zai gayawa magoya bayansa cewa shi ya cika alkawarin da yayi lokacin neman zabe ya kuma fada masu bisa ga tsarin kasar dole ne su bi umurnin kotu. Idan ko ya sabawa umurnin Kotu majalisa na iya tsigeshi.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG