Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Tarayya Ta Dutse Ta Yaye Dalibai Kusan 1000


Bukin yaye dalibai na Jami'ar Tarayya dake Dutse a Jihra Jigawa
Bukin yaye dalibai na Jami'ar Tarayya dake Dutse a Jihra Jigawa

A watan gobe ne ake sa ran cewa, rukunin daliban Jami'ar Jigawa dake nazari da koyon aikin likita zasu fara shiga Asibiti domin Atisaye kan yadda ake duba marasa lafiya a aikace.

Jami’ar tarayya ta Jigawa wace ke garin Dutse kuma ke cikin jerin Jami’o’I 9 da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa a shekara ta 2011, ta yaye dalibai sama da 900 wadanda ke nazari a fannonin ilimi daban-daban a matakin digiri na daya da na biyu.

A bukin yaye daliban Jami'ar karo na biyar wanda akayi a ranar Asabar din da ta gabata, jami'ar ta yaye dalibai 786, daga cikin su, dalibai 52 sun sami digiri mai daraja ta daya.

Ko da yake, har yanzu ba a tantance asibitin da daliban jami'ar da suka nazarci aikin likita zasu yi amfani da shi wajen koyon aikin likita a aikace ba, a cewar shugabar jami'ar Farfesa Fatima Batul Mukhtar.

A saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

JAMI'AR TARAYYA TA JIGAWA CE TA FI HABBAKA
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG