Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Difilomasiyyar Amurka da Masar za su gana


John Kerry, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry zai tattauna tsaro da jami’an Masar a tsakanin yau da gobe.

Wannan ziyarar matashiyar ziyarar kasashe 5 ne a Gabas ta Tsakiya da kuma Kudu Maso Gabashin Asia. Wani babban ofishin harkokin wajen Amurka yace Amurka ta damu da yadda ake ta kai jerin hare-hare a yankin Sinai.

Wanda ‘yan kungiyoyin ta’adda masu alaka da ISIS ke daukar alhakin. Sanarwar da ta fita a jiya Juma’a tace, Masar na fuskantar barazanar ‘yan ta’addar da ke da alaka da ISIS.

Mista Kerry zai gana da Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry da shugaban kasar Abdel Fatah El-Sisi game da tsaron kasar. Daga karshe Amurka da Masar zasu tattauna maganar Siyasa, ‘yancin Bil’adama da maganar tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG