Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyya Mai Mulkin Ethiopia Tana Murnar Samun Nasarar Zabe, Yayin Da Tarayyar Turai Ta Ce Da Alamun Magudi


Jami'an zabe su na rufe akwatin kuri'a a bayan da aka kammala jefa kuri'a a wata rumfar zabe a Addis Ababa ranar Lahadi, 23 Mayu 2010.
Jami'an zabe su na rufe akwatin kuri'a a bayan da aka kammala jefa kuri'a a wata rumfar zabe a Addis Ababa ranar Lahadi, 23 Mayu 2010.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce tana da damuwa game da zaben da aka gudanar ranar lahadi a kasar Ethiopia, yayin da dubban magoya bayan jam'iyya mai mulkin kasar suka yi gangamin murna yau talata.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce tana da damuwa tattare da zaben da aka gudanar ranar lahadi a kasar Ethiopia, wanda jam'iyya mai mulkin kasar ta lashe da gagarumin rinjaye.

Hukumar zabe ta kasar Ethiopia ta ce gamayyar jam'iyyun EPRDF ta lashe kujeru 477, kimanin kashi 87 cikin 100 na kujerun majalisar dokokin kasar. Dubban magoya bayan EPRDF sun yi gangami yau talata a birnin Addis Ababa domin murnar wannan nasara.

Amma kungiyar 'yan kallon zabe ta Tarayyar Turai ta ce ta ga ana amfani da albarkatun gwamnati wajen taimakawa jam'iyya mai mulkin kasar a lokacin yakin neman zabe.

Babban jami'in 'yan kallon, Thijs Berman, ya ce sun kuma samu rahotanni na cin zarafi da kuntata ma abokan hamayya. Ya ce yawan koke-koke da suka samu, kuma ganin cewa kusan duk iri daya ne, ya haifar da damuwa.

Shugabannin babbar gamayyar hamayya da ake kira Medrek ta yi tur da sakamakon zabena zaman na bogi kawai. 'Yan hamayyar suka ce jam'iyya mai mulkin kasar ta kanainaye dukw asu ayyukan da suka shafi zaben daga farko har karshensa.

Hukumar zaben Ethiopia ta ce an yi wannan zaben tsakani da Allah kuma ta hanyar dimokuradiyya.

XS
SM
MD
LG