Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar PDP Ta Kalubalanci Gwamnatin Jahar Kaduna


PDP

Saboda jam’iyya ta rasa zabe ba shine zai sa a zauna ayi shiru ba

Jam’iyyar PDP, a jahar Kaduna, ta ce gwamnatin jam’iyyar APC, a jahar ta rasa manufa shi yasa ta gaza yin abun a zo a gani shugaban kungiyar shuwagabanin kananan hukumomi na jam’iyyar PDP,a jahar Kaduna kuma shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Kaduna ta arewa Malam Abdullahi Aliyu Babawo, ne ya gayawa manema labaru jim kadan bayan wani taro a garin Kaduna cewa PDP, ba zata rugume hannu tana gani a nayin abunda bai dace ba ga alumar jahar ba.

Ya ce saboda jam’iyyar ta rasa zabe ba shine zai sa a zauna ayi shiru ba rasa zabe ma zai sa yanzu mu tashi muyiwa mutane aiki.

Gwamnan jahar Kaduna ya fito da wasu kudirori nashi wanda yake ba dai dai yake da abunda talakan jahar Kaduna yake so ba, ya ce babu maganar zama dan jahar Kaduna, na nuna cewa da Igbo da Bayarabe duk wani wanda ya shigo Kaduna ya zama dan jahar Kaduna, ba zai yuba saboda wani kudiri nashi na yana so ya zama shugaban kasa yazo yana takurawa talaka.

Yanzu idan dan jahar Kaduna na neman dan Sanda toh yanzu dashi da Bayarabe duk zasu ta gwagwagwa saboda haka wannan baza mu yaeda ba kuma dole mu kira mutane a tashi tsaye dan a yaki wanna abu.

Saida duk da wadannan korafe korafe mai Magana taimakawa Gwamna El Rufai ta fuskar yadda labaru Mr. Samuel Aruwan, ya ce ba zasu tsaya chachar baki da jam’iyyar PDP, ba wadanda zasu yake hukunci talakawan jahae Kaduna ne.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG