Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Ta Lallasa Brazil a Wasan Kwallon Cin Kofin Duniya


'Yan wasan Brazil da Jamus

A wani abun da bai taba faruwa ba Jamus ta lallasa Brazil a wasan kwallon kaafa na cin kofin duniya da ake yi yanzu a kasar ta Brazil

:

Kasar Jamus tayi wasan kwallo maikayatarwa da ban mamaki inda ta nuna kwarewa da bajinta a tarihin gasar kwallon kafa na cin kofin duniya, inda ta lallasa Brazil a wasan kusa da karshe da ci 7-1. Ta sami nasarar shiga zagayen karshe domin daukar kofin duniya.

Yawan kwallo da Jamus ta jefa a raga shine mafi yawa da wata kungiyar kwallon kafa ita kadai ta jefa a ragar wata a wasan kusa da na karshe a tarihin gasar cin kofin duniya.

Wannan ne kuma karo na farko cikin shekaru 80 da wata kasa zata jefa kwallo bakwai a ragar Brazil.

Jamus ta jefa kwallo sau biyar a ragar Brazil cikin rabin sa’a da fara wasan da aka yi jiya talata a filin wasan da ake kira Estadio Miniero.

Yau ne kasar Netherlands zata kara da Argentina domin tantance kasar da zata fuskanci jamus.

XS
SM
MD
LG