Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Japan Tana Amfani Da Jirage Masu Saukar Ungulu Kan Masana'antun Nukiliyarta


Hoto daga tashar talabijin ta Japan, dake nuna jirage masu saukar ungulu suna zuba ruwa kan cibiyoyin Nukiliyar kasar da suka lalace.
Hoto daga tashar talabijin ta Japan, dake nuna jirage masu saukar ungulu suna zuba ruwa kan cibiyoyin Nukiliyar kasar da suka lalace.

Jami’an kasar Japan sun tura jiragen sama masu saukar ungulu domin su zubawa masana’antar nukiliyar Fukushima ruwa a kokarin sanyanya injunan sarafa makamasin nukiliya a cikin masana’antar.

Jami’an kasar Japan sun tura jiragen sama masu saukar ungulu domin su zubawa masana’antar nukiliyar Fukushima ruwa a kokarin sanyanya injunan sarrafa makamasin nukiliya a cikin masana’antar.

Jami’an suna kokarin rigakafin bala’in turiri mai guba fitowa daga rodin injunan sarrafa makamashin nukiliya. A yau alhamis gidan talibijin na Japan ya nuna hotunan jiragen sama masu saukar ungulu suna zubawa masa’antar ruwa.

Haka kuma jami’ai sunce sun girka manyan motocin daukan ruwa domin kokarin fesawa injunan sarrafa makamashin ruwa daga kasa. Wani lokaci a yau alhamis za’a fara kokarin maida wutar lantarki a masana’antar.

Fadar shugaban Amirka tace shugaba Barack Obama na Amirka yayi tayin taimakon Amirka a zantawar da yayi ta wayar tarho da Prime Ministan Japan Naoto Kan, da sanyin safiyar yau alhamis, Shi kuma shugaban hukumar kula da makamashin nukiliyar Amurka, Gregory Jackzko, yace akwai mummunar hatsarin dake tattare da turiri mai guba dake fitowa a sakamakon lalacewar masanantar nukiliyan Japan, a saboda girgizar kasar data auku a kasar.

A jiya Laraba Mr Jackzko, yayi wannan furucin a Majalisar dokokin Amirka. Yace tana yiwuwa babu sauran ruwan da zai sanyaya rodin makamashin a wani bangare na masa’antar. Yace akwai kuma inda kila yake yoyon ruwa. Haka kuma Mr. Kackzko yayi gargadin cewa na’urar sanyaya rodin a wani bangare na masa’antar aikin samar da wutar lantarki ya mutu, hakan na nufi zaiyi wuya a gyara ta idan ta lalace.

Galibi rodin makamashin nukiliya kan yi makonni ko watanni suna da zafi koda ba’a yi amfani dasu ba. Ba tare da samun ruwan sanyaya su ba, suna iya narkewa su fitar da turiri mai guba mai yawan gaske cikin yanayi.

A halin da ake ciki kuma ofishin jakadancin Amirka a Tokyo yayi wa Amerikawa kashedin cewa su nisanci masa’antar nukiliyan data lalace da nisan akalla kilomita tamanin, yayinda ita kuma gwamnatin Japann ta yiwa al’ummarta kashedin cewa su nisanci masa’antar da nisan kilomita talatin.

A yau alhamis ne kuma ake sa ran babban direktan hukumar makamashin atom ta kasa da kasa Yukiya Amano, zai isa Japan domin zantawa da manyan jami’an kasar akan irin taimakon da hukumarsa zata iya bayarwa.

A wani labarin kuma, ana fuskantar karancin kayayyakin abinci da mai da kuma ruwa a yankunan da suka fi dandanawa a yayinda ake ta baiyana tsoron samun kari da bazuwar turiri mai guba daga masa’antar nukiliyan Fukushima data lalace.

Wakilan Muryar Amirka a Japan, sun bada rahoto a jiya Laraba cewa iyalai da masu aikin ceto yanzu basu samun komai illa buraguzanan gine gine. Sa’anan kuma, tituna kusan fayau suke domin ana karancin mai, saboda direbobi sun gwamace su nisanci masana’antun da suke fitar da turiri mai guba.

XS
SM
MD
LG