Accessibility links

Jihar Ekiti ta ba kamfanin kasar sin kwangilar gina tagwayen hanyoyi daga Ikere Ekiti zuwa babban birnin jihar Ado Ekiti

Gwamnatin Jihar Ekiti ta ba kamfanin kasar Sin kwangilar gina tagwayen hanyoyi daga Ikere Ekiti zuwa Ado Ekiti babban birnin jihar.

Gwamnan Jihar Kayode Fayemi shi ya sa hannu a kwangilar a madadin gwamnati. Kwangilar zata ci miliyoyin nerori. Yayin da yake jawabi gwamnan ya ce idan aka fadada hanyar zata taimaka wurin inganta tattalin arzikin jama'ar jihar da jin dadin rayuwarsu. Gwamnan ya bukaci jama'ar jihar su goyi bayan shimfida tagwayen hanyoyin. Shi ma mataimakin shugaban kamfanin cewa ya yi jama'ar jihar zasu samu alfanun hanyan.

Kamafanin zai fara aikin gina hanyoyin ba tare da bata lokaci ba. Haka kuma kamfanin zai gina hanyar ba da karba ko kwabo ba. Za'a kammala aikin cikin watanni goma sha biyu. Gwamnatin jihar zata biya kudin gina hanyar nan da shekaru goma.

Hassan Umaru Tambuwal nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG