Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JIHAR NEJA: Baraka Tsakanin Gwamna da Dan Majalisar Dattawa daga Jihar


Wata baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan jihar Neja da kuma dan majalisar dattawa mai kilitar gabashin jihar.

Gwamna Abubakar Sani Bello da dan majalisar dattawa Barrister David Umar sun shiga wata takunsaka.

Wasu jaridun Najeriya sun ambato Sanata David Umar yana sukar lamirin Gwamna Abubakar Sani Bello akan yadda yake raba mukamai a jihar musamman sakataren gwmnatin jihar da ya fito daga bangare guda da gwamnan.

Kakakin gwamnan Dr Ibrahim Doba ya basu umurnin su sawa bakinsu linzami akan batun. Amma shugaban APC na jihar Injiniya Muhammad Imam yayi tsokaci akan lamarin.

Dattawan jam'iyyar APC sun kafa wani kwamiti saboda sasanta manyan da yanzu rikici ya kunno kai tsakaninsu.

Wani dattijo yace hakuri da kai zuciya nesa shi ne maganin abun. Batun kace na ce da gwamna bai ma taso ba idan aka yi hakuri.

Ga rahoton Nasiru Basari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG