Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JIHAR SOKOTO: Sai da Takardar Shaida Za'a Bayar da Dakin Kwana a Otel


Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Saboda tabarbarewar tsaro a Najeriya gwamnatin Sokoto ta kafa dokar hana ba kowa dakin kwana a kowane otel ba tare da cikakkiyar takardar shaida ba

Sabuwar dokar ta zama wajibi idan aka yi la'akari da yanayin tabarbarewar harkokin tsaro a kasarduk da zaman lafiyan da jihar take ciki.

Imam Imam mai ba gwamnan shawara akan lamuran labarai ya bayyana dalilin kafa dokar. Yace abun mamaki ne a ce tuntuni babu irin wannan dokar. A koina a duniya idan mutum ya je otel sai ya bayar da fasfo nashi da wata shaida kafin a bashi daki. Ko dan kasa ne sai ya bayar da shaidar ko shi wanene.

Masu otel otel a jihar sun yi na'am da sabuwar dokar wacce suka ce ba sabuwar abu ba ce a wasu sassan duniya. To amma suna ganin akwai wani kalubale da yakamata gwamnati ta fuskanta saboda tabbatar da dokar ta yi aiki.

Aliyu Dankani manajan babban gidan saukar bakin Dankani dake Sokoto yace sun kai shekaru 20 suna aikin otel a Sokoto amma basu taba ganin wata kungiya ba da zata tabbatar an gudanar da wata doka. Dangane da wannan sabuwar dokar ba'a san irin tanadin da gwamnati ta yi ba.

Kamata yayi a tara masu otel a yi kungiya saboda baki ya zo daya akan tabbatar da yin aika kafada da kafad da gwamnati wurin aiwatar da dokar.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG