Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Alhazan Ghana Na Farko Ya Tashi Yau Da Safe


Alhazan kasar Ghana sun fara tashi zuwa kasar Saudiyya.

Mataimakin shugaban kasar Kwesi Amissah-Arthur ne ya wakilci shugaba John Dramani Mahama a wurin kaddamar da tashin jirgin alhazan na farko

Da misalin karfe biyar na safiyar talatar nan agogon kasar Ghana, rukunin alhazan farko ya tashi zuwa kasar Saudiyya a gaban mataimakin shugaban kasar ta Ghana Kwesi Amissah-Arthur. Shugaban hukumar alhazan kasar Ghana alhaji Tanko ya tabbatarwa wakilin Sashen Hausa a birnin Accra, Baba Yakubu Makeri cewa sun kammala shirye-shirye tsaf a Ghana da kuma can kasar Saudiyyar, har wa yau ya ce sun dauki matakan kare lafiyar Mahajjatan kasar game da wani ciwon da hukumomin kasar ta Saudiyya suka ce ya bulla. Ga Baba Yakubu Makeri da cikakken rahoton:

Jirgin Alhazan Ghana na farko ya tashi - 2:45
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG