Accessibility links

Wani jirgin ruwa shake da man fetur da aka sato ya nitse cikin teku a wajejen kudu maso yammacin Najeriya.

Wani jirgin ruwa dauke da man fetur da ake zato na sata ne ya makale cikin teku kusa da jihar Bayelsa a Najeriya.

Jirgin wanda ya cika makil da man fetur ya nitse a cikin tekun nahiyar Naija Dalta. Lamarin ya auku ne da yammacin jiya Litinin yayin da ya yi dakon man da ya wuce kima. Lautenan Kanal Onyema Nwachukwu kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwa dake lura da yankin ya tabbatar da nitsewar jirgin ya kuma ce sun aika da jami'ansu domin su ceto jirgin. Jami'in ya ce bisa ga abun da suka gano jirgin na dauke ne da man sata. Amma duk da haka zasu cigaba da bincike kana su shaidawa manema labarai abun da suka gano.

Wani dake nazari kan satar mai Malam Ibrahim Umar ya yi addu'ar Allah ya baiwa rundunar sa'a wurin ceto jirgin amma musamman wajen gano wadanda ke da hannu cikin wanna ta'sar ta satan dimbin mai. Ya ce matsalar satar mai na karya tattalin arzikin kasa. Malam Umar ya ce idan an bar jami'an tsaro zasu yi aikinsu to amma abun takaici shi ne lokacin da suke bincike sai ka ga an bugo waya daga sama a ce su bar binciken ko kuma su saki wadanda suka kama. Ya ce wadanda suke tare da man ai basu ba ne da man. Akwai wasu manya a bayansu da suka sasu yin aikin. Su ne ya kamata a bankado kana a cafkesu. To amma manya manyan mutane ne da suke a Abuja masu rigar kariyar gwamnati da babu wanda ya isa ya tabasu. Wannan lamarin shi ne matsalar kasar-wato barin wasu su fi karfin dokar kasar.

Dama can satan danyen man fetur a Naija Dalta ba wani sabon abu ba ne. Abu ne wanda ya yiwa kasar katutu har ma tafi kowace kasa a duniya fuskantar satar danyen mai. Jami'an tsaro sun ce suna kama masu laifin satar amma sai a sakesu ba tare da saninsu ba.

Lamido Abubakar nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG