Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Goodluck Jonathan Ya Zabi Mohammed Namadi Sambo A Matsayin Mataimakinsa


Architect Mohammed Namadi Sambo

Sabon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya zabi gwamna Mohammed Namadi Sambo na Jihar Kaduna a matsayin wanda yake son ya zamo mataimakinsa.

Sabon shugaban Najeriya ya zabo mutumin da yake son ya zamo mataimakinsa daga yankin arewacin kasar inda Musulmi ek da rinjaye.

Kafofin labarai sun ce shugaba Goodluck Jonathan ya zabi gwamna Mohammed Namadi Sambo na Jihar Kaduna domin ya ba wannan mukamin a bayan da ya shafe daren laraba yana tattaunawa da gwamnonin kasar a Abuja, babban birnin tarayya.

Har yanzu dai shugaban bai ce uffan ba a game da wannan zabi na sa. A yanzu tilas sai majalisar dokoki ta amince da Sambo kafin ya zamo mataimakin shugaban.

Sambo, wanda injiniyan zana gine-gine ne, ya yi aiki ma gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu a can baya. Ya taimaka wajen bunkasa noma a Jihar Kaduna, ya kuma inganta samar da ruwa da lantarki a yankin.

Zaben Namadi Sambo ya maido da daidaiton addini da na yanki a shugabancin kasar. A bisa al'ada, jam'iyyar PDP ta shugaba Jonathan tana tsarin karba-karba na kujerar shugabancin kasar a tsakanin kudancin Najeriya inda Kirista ke da rinjaye, da kuma arewacin kasar inda Musulmi suka fi yawa. Idan an zabi shugaba dan kudu, to mataimakinsa dan arewa ne, haka kuma idan shugaba Kirista ne, to mataimakinsa Musulmi ne.

Har yanzu akwai ayar tambaya a kan ko wanene zai tsaya takarar shugaban kasa ma jam'iyyar PDP a zaben 2011. Wani mukarrabin shugaban ya fada laraba cewa yana fata Jonathan zai yi takara a zaben. Sai dai kuma yin takararsa a zaben na 2011 na iya janyo fitina.

Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa, Musulmi daga arewacin Najeriya, ya rasu shekaru biyu da rabi da hawa kujerar mulki a wa'adin da aka yi tsammanin zai dauke shi shekaru 8 a wanan gurbi na 'yan arewa.

Wasu jami'an jam'iyyar PDP sun ce ya kamata shugaban kasar na gaba shi ma ya fito daga arewa, kuma har wasu 'yan takara da yawa daga arewacin kasar sun nuna sha'awar tsayawa takara a 2011.

XS
SM
MD
LG