Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada Mu Yarda Bambancin Siyasa Yasa Mu Juyawa Juna Baya


Hillary da Bill Clinton
Hillary da Bill Clinton

Tsohuwar ‘Yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton tace a shirye take ta shiga cikin tattaunawar da jama'a ke yi kan sauyin yanayin siyasa a Amurka tun bayan zaben shugaban kasa da akayi a watan Nuwamba.

Clinton ta fada jiya jumma'a a wajen taron liyafar cin abincin dare ta 19 ta bukin Saint patrick Kungiyar Mata Jinsin kasar Ireland a birnin Scranton dake Jihar Pennsylvania, cewa, “Kamar yawa yawan abokaina a yanzu, yana zamar min wahala in kalli labarai.”

Amma duk da haka Clinton ta kara da cewa “Ban yarda “cewa zamu iya barin banbancin ra’ayin siyasa ya zamo abinda zai raba kawunanmu ba, bai kamata mu yi watsi ko mi juya ma juna baya ba a saboda kawai muna da bambancin siyasa. Tilas “mu saurari junanmu, domin mu karu da juna.”

Clinton tace “Na shirya in fito daga sako domin in haska fitila akan abinda yake faruwa acikin dakunan girkin mu zuwa teburan cin abincin mu, hakan zai kara mana karfi da kuma baiwa kowa kwarin gwiwa na cigaba da tafiyar.”

Ana yada jita jitar cewa tana tunanin tsayawa takarar Magajiyar garin New York, amma mataimakanta sun ce ba haka abin yake ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG