Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A wani yunkuri na bazata kamfanin Shell ya amince ya biya mutanen da aka gurbatar da muhallinsu a yankin Neja Deltan Najeriya

Wani reshen kamfanin Royal Dutch Shell ya biya adadin kudaden fansa da ake kyautata zaton sune mafi girma da kamfanin ya biya jama’ar da aka gurbatawa muhalli sakamakon ambaliyar danyen mai a Najeriya.

Yau Laraba ne kamfanin Shell ya amince akan cewa zai biya dala dubu uku-uku ga mutane su fiye da dubu 15 a garin Bodo dake kudancin Najeriya, dangane da abunda kamfanin ya kira lamarin da-na-sani na gurabata musu muhalli a shekara ta 2008.

Adadin kudin da kowani mutum daya ya samu yayi dai-dai da karamin albashi da ake biyan ma’aikata a Najeriya na tsawon shekaru 3.

Kudaden fansan wadanda idan aka tara jimlarsu baki daya zasu kama dala miliya 83 da dubu dari 5, biyansu zai kawo karshen shekaru 3 da aka kwashe ana shari’a, kuma akwai karin dala miliyan 30 da kamfanin zai karawa al-ummar da ambaliyar man ya shafa a wannan yanki.

Wadannan kudade sun gaza adadin da lauyoyi suka nema, wato dala miliyan dari 4, amma sun dara misalin dala dubu shida-shida da kamfanin yayi kokarin baiwa al-ummar daga farko domin sulhuntawa.

XS
SM
MD
LG