Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Kamaru da Kokarin Dakile Yaduwa Kafofin Sadarwar Zamani


Shugaban Kamaru Paul Biya

Anfani da kafofin sadarwar zamani na duniyar gizo (da a turance ake kira “social media”) tana kara habaka a kasar Kamaru; haka ma kokarin da gwamnati keyi domin sa ido akan yadda ake anfani da ita

Wadanan ‘yan majami’ar cocin Presbytarian Bota a lardin Limbe dake kudu maso yammacin Kamarune suke yiwa wasu mutane uku addu’a ne wato Fomusoh Ivo Feh da Afuh Nivelle Nfor da kuma Azah Levis.

Wadannan mutanen uku wata kotun soja ce ta yanke masu hukumcin dauri wannan watan bayan an samesu da laifin aika sakon ba’a ta kafar sadarwar SMS wai zasu daukawa kungiyar ta’adanci ta Boko Haram mayaka.

Yayinda ake yi masu shari’a ba’a bar ‘yan kallo sun shiga kotun ba, lamarin da ya sa kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International da sauran kungiyoyin ‘yan rajin kare hakkin bil Adama suka yi tur da hukuncin.

Cikin wadanda suka hallara a cocin akwai Tabot Timothy dan shekaru 22 da haihuwa wanda dalibi ne dake nazarin fannin shari’a a Jami’ar Douala ta Kamaru

Timothy yana cewa: “Ya dace a gudanar da binciken kwakwaf domin a tabbatar cewa wadannan mutanen ba’a su keyi. Yin hakan yana bisa Gaskiya. Amma ba’a gudnar da cikakken bincike ba akan wadanda aka yiwa hukunci”

Gwamnatin Kamaru ta jima tana anfani da dokoki daban daban da suka hada da dokar yaki da ta’addanci ta shekarar 2014 da dokar laifuka da aka sake sabuntawa domin bin digdigin sakonni ko bayanan da jama’a ke aikawa ta wayar tafin hannu da yanar gizo.

Wani lauya mai suna Barrister Geroge Marcelli Tsoungui (Tsongi) dake cikin Kungiyar Lauyoyin Kamaru yayi sharhi cikin harshen Faransanci akan lamarin, yana cewa:

Lauya Tgsoungui (Tsongi) yace hukuncin wata shida zuwa shekara biyu da tarar dalar Amurka dubu goma zuwa dubu ishirin ne za’a yiwa duk wanda aka samu da laifin yada labaran karya ta kafar sadarwar zamani. Yace ana iya ma ninka hukuncin sau biyu idan aka gano labarin da aka yada an yi ne da nufi tada zaune tsaye cikin jama’a.

A watan Janairun wannan shekarar ne ‘yansanda suka tsare wani dan jarida bayanda ya bada rahoto ta kafar sadarwar zamani bisa kuskure cewa Shugaba Paul Biya ya ziyarci wata rundunar sojoji a arewacin kasar.

A watan Maris ma ‘yansanda sun cafke mutanen da ake zargi da tsegunta abun dake cikin wata wasikar siri a kafar sadarwar zamani. Wasikar ta fito ne daga ministan tsaron kasar inda yace ‘yan Boko Haram sun shiga Birnin Yaounde.

Sai dai kuma duk da yawan kame-kamen da a keyi, kafofin sadarwar zamani sai karuwa su keyi a Kamaru kuma ‘yan adawa da masu goyon bayan gwamnati suna anfani dasu – kamar yadda wani masanin fannin hanyoyin sadarwa din, Nelson Tawe yake bayyanawa:

Nelson Tawe ke nan yake cewa:“babu yadda za’a gujewa anfani da kafofin sadarwa irin wadanan. Da wuya a dakile kafofin. Kokarin dakilesu kamar sa ruwa ne a kwando. Wadannan kafofin sun kafu kuma babu yadda za’a toshe bakinsu. Gwamnati nada jan aiki a kokarinta na neman dakilesu, inji Tawe. END

Kasar Kamaru ba ita kadai bace kasar da ta damu da yaduwar wannan hanyar sadarwar ta duniyar gizo.

Kasashen Afirka da dama sun dauki irin matakan da Kamaru ta dauka domin wani sabon rahoto da wata kungiya dake Washington da ake kira Freedom House ta fitar, tace ‘yancin yanar gizo ya ragu ainun cikin shekaru shidan da suka gabata a duk fadin duniya.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:16 0:00

XS
SM
MD
LG