Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Kamaru Ta Fara Yakar Yaduwar Makamai A Cikin Kasar


 Paul Biya, shugaban kasar Kamaru
Paul Biya, shugaban kasar Kamaru

Sojojin Kamaru sun gano bindigoji da albarusai da adduna da wukake a wani dakin ajiyar kaya kusa da babban birnin kasar Yaounde

Kasar Kamaru ta fara farautar makamai da suke yaduwa a cikin kasar, yayin da kuma take yaki da kungiyoyi biyu masu tada kayar baya,lokacin da kuma take kuma shirin gudanar zaben kasa bana. Wakilin Muryar Amurka Moki Edwin ne ya aiko da wannan rahoto daga garin Awae, inda sojoji suka ce sun gano makamai da aka shigo dasu ta barauniyar hanya masu tarin yawa a wani dakin ajiyan kaya kusa da babban birnin kasar, Yaounde.


A cikin dakin ajiyan kayar, sojojin sun gano albarusai dubu goma da 500 da wasu nakiyoyi da ba a bayyana adadinsu ba da bindigogi da adduna da kuma wukake. Wadanda aka kama zuwa yanzu danagne da makaman 'yan Kamaru ne.


Jami’ai suna zaton an shigo da makamai ne ta kasa daga kasashe makwabta, musamman Najeriya. Sai dai mazauna yankin sun bayyana al’ajabinsu ga yanda aka shige shingayen yan sanda da jami’an tsaron genderma aka shigo Awae da makaman.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG