Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Saudiya Ba Zata Cire Hannunta daga Shirya Aikin Hajji Ba


Sarki Salman na Saudiya

A jiya Litinin Sarkin Salman na Saudiya ya ki amincewa da maganar cewa kasarsa ta saduda da maganar matsayinta na tsara aikin Hajji, biyo bayan turmutsutsun da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mahajjata.

Sarkin na Makka yace, wannan zance ne na rashin sanin ya kamata, sannan maganar cewa kasar Saudiya ba zata iya kula da mahajjata ba, ba zai shafi tsara hajjin shekara-shaekarar da kasarsa ta ke yi ba.

Hatsarin turereniyar dai ya faru ne a ranar 24 ga Satumbar da ya gabata a lokacin da wasu sahun mahajjata suka hade da juna a wajen jifan shedan. Gwamnatin Saudiyya ta bada sanarwar mutuwar mutane 769.

Amma kamfanin dillancin labarai na AP yace, mutane 1,480 ne suka halaka a wajen, wanda in haka ne zai zama hatsarin aikin hajji da ya fi kowanne haifar da mutuwar alhazai.

Shugaban Iran ya zargi Saudiya da rashin iya tsara hidimar aikin hajji da kuma rashimn cancantarta, a yayin da babban jagoran musulunci na Iran yace, ya kamata kasashen musulunci su fara daukar nauyin tsara aikin hajjin.

Iraniyawa 465 ne suka mutu a Makka din, a yayin da Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fidda sanarwa a jiya cewa alhazansu guda 181 ne suka mutu, sannan guda 53 sun bace.

Sarkin dai a watan da ya gabata ya bukaci a bashi rahoton yadda ake tsara aikin hajjin kasar.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG