Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afrika na bukatar kula dangantaka da kasashe masu arziki

Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar na nuni da cewa, kasashen nahiyar Afrika suna bukatar kulla dangantaka da kasashe masu bunkasar tattalin arziki domin samun bunkasar tatalin arziki mai dorewa.

Rahoton da aka gabatar jiya Litinin, ya ce kasashen nahiyar Afrika suna kara cudanya da kasashe masu karfin tattalin arziki. Rahoton ya kuma kara da cewa, dangantakar cinikayya da kasashe dabam dabam zai taimakawa nahiyar.

Kasashe masu arziki, kamar China da Indiya da Koriya ta Kudu da Brazil da kuma Turkiya zasu iya taimakawa wajen samar da ilimin fasaha da harkokin raya kasa da zasu taimaka wajen inganta rayuwar miliyoyin mutanen nahiyar Afrika.

Wannan rahoton na hadin guiwa ne tsakanin Majalisar Dinkin duniya da bankin raya kasashen Afrika da kuma kungiyar bunkasa tattalin arziki da yin mu’amala.

XS
SM
MD
LG