Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwa: Kasuwar Kayan Lambun Unguwar Asokoro, Abuja


Shirin Kasuwa na wanna makon ya kai ziyara wata kasuwar kayan lambu da ke kan titin JC Junction a unguwar Asokoro a cikin garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

A wata hira da Murtala Abdullahi Muhammed wani dan kasuwar da ke amfani da na'urar POS, ya ce wannan dabarar ta samo asali ne daga tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya kuma Tsohon Sarkin Kano mai murabus Muhammadu Sanusi na biyu, wanda ya yi magana akan yadda za a rage hada-hadar kudi a hannu mutane.

Ko da yake a lokacin an yi wa tsarin kallon wani abu mai wuya, amma yanzu kuma suna ganin saukinsa, a cewar Abdullahi. Ya kara da cewa amfani da wannan na'urar ta taimaka wajen rage cunkoso a bankuna musamman a lokacin da ake fama da annobar coronavirus.

Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu Elhikaya, ya kuma yi hira da wasu 'yan kasuwar ta kayan lambu da ke unguwar Asokoro.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

Kasuwa: Kasuwar Kayan Lambun Unguwar Asokoro, Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:00 0:00


XS
SM
MD
LG