Accessibility links

Ra'ayoyi sun sha bamban, wasu na cewa Argentina ce za ta yi nasara, wasu na cewa sam Jamus dai!

'Yan sa'o'i kalilan kafin a buga wasan karshe a gasar cin kofin kwallo kafa na duniya tsakanin Argentina da Jamus a Rio de Janeiro wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Sakkwato, Murtala Faruk Sanyinna ya shiga gari ya tattauna da masu sha'awar wasan kwallon kafa, kowannen su yayi bayani gami da yin hasashe akan yadda wasan zai kaya:

Waiwaye aka ce adon tafiya, Murtala Faruk Sanyinna ya waiwaya, ya koma da mu baya can cikin tarihin wasannin karshen da aka taba karawa tsakanin Argentina da Jamus a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya:

Yanzu haka dai hankulan jama'a sun koma kan wasan na karshe wanda za a buga nan da 'yan mintoci kalilan a birnin Rio de Janeiro.

XS
SM
MD
LG