Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa ta Ja Kunnuwan Koriya ta Kudu tare da Damarar Yaki


Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Cikin 'yan kwanakin nan kasashen Koriya ta arewa da ta kudu sun sha musayar harbe harbe lamarin da ya sa yanzu Koriya ta Arewa ta ba makwafciyarta har zuwa gobe.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya saka dakarun kasar cikin shirin ko ta kwana, ya kuma ayyana "kwariya-kwariyar yaki" a yankunan kusa tudun na tsaira tsakaninta da makwabciyarta, Koriya ta Kudu.

Yau Jumma'a ce shugaban ya dauki wannan mataki.

Kamar dai yadda kamfanin dilancin labarai na kasar ya bayyana, bayan majalisar tsaron kasar ta kammala taronta, Mr Kim yace dakarun kasar da suke sahun gaba "su kasance cikin shirin yaki", daga karfe biyar na yamacin yau agogon kasar.

Hukumomin kasar a Pyongyang sun sha daukan irin wanan mataki a baya lokacin da aka sami rashin jituwa da makwabciyarta a shekarun 2010, da kuma 2013.

Jakadan Koriya ta Arewa a Beijing can kasar China ya kira taro da manema labarai a yammacin yau, inda ya sake nanata gargadi kan wa'adin da kasar ta bayar da zai kare gobe Asabar. Yace Koriya ta Arewa kasa ce mai fada da cikawa.

Da aka tambayeshi matsayar China kan wannan mataki, yace tambayar bata da ma'ana.

Ya kara da cewa "idan makiyi yayi kunnen kashi da kashedi da muka yi, babu makawa zamu dauki mataki.. Sojojinmu basa soki burutsu. Inji jakada Ji.

Kasashen biyu dai sun yi musayar harbe harbe kodashike babu wani rahoto kan an sami hasarar rayuka.

XS
SM
MD
LG