Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa tayi wani gagarumin faretin soji


Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Il da dansa Kim Jong Un, a cikin wannan hoton da kamfanin dillancin labarai na Koriya ya fitar ranar laraba 6 ga watan Oktoba. 2010,

Dan shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Il, wanda aka zaba ya gaji mahaifinsa, ya yi wata muhimmiyar fita irinta ta farko a bainin jama’a.

Dan shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Il, wanda aka zaba ya gaji mahaifinsa, ya yi wata muhimmiyar fita irinta ta farko a bainin jama’a, a wani faretin soji mafi girma da aka yi cikin shekaru da dama a kasar. Kim Jong Un dan shekaru 27, ya bayyana tare da mahaifinsa Kim Jong Il yau lahadi inda suka jagoranci faretin cika shekaru 65 da mulkin jam’iyar kwaminis a kasar. Dubban dakaru suka yi maci kan titunan Pyongyong ‘yan kallo suna shewa. An yayata faretin kai tsaye a tashar talabijin ta kasar, wani abinda ya zama ba saban ba a koriya ta arewa, inda hukuma take sa ido ainun kan shirye shiryen da za a yayata. Paretin ya kunshi nune nune iri iri, da dubban tankokin yakin, da makamai masu linzami da kuma sauran makamai. Makon da ya shige ne aka tabbatar da Kim Jong Un a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa.

XS
SM
MD
LG