Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ECOWAS Ta Ce A Oktoba Zata Yanke Hukumci Kan Karar Hissene Habre


Kungiyar Tarayyar Afirka tana cikin wadanda suka bukaci Senegal ta gurfanar da tsohon shugaban Chadi, Hissene Habre, a gaban kotu bisa zargin kashe dubban abokan hamayyar siyasa lokacin da yake mulki.

Kotun zata yanke hukumci a kan ko kasar Senegal tana da hurumin gurfanar da tsohon shugaban na Chadi gaban kotu bisa zargin cin zarafin bil Adama da kashe dubban 'yan hamayya.

Kotun Tarayyar Afirka ta Yamma dake zama a Abuja, babban birnin Najeriya, ta ce a cikin watan Oktoba zata gabatar da hukumci a kan ko kasar Senegal tana iya yin shari'ar tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre, bisa tuhumar cin zarafin bil Adama da kashe dubban 'yan hamayya a lokacin da yake mulkin kasar cikin shekarun 1980.

A shekarar 2008 neHabre ya shigar da kara gaban kotun Tarayyar Afirka ta Yamma, ECOWAS, domin ta hana kasar Senegal gurfanar da shi gaban shari’a. A ranar jumma’a a Abuja, kotun ta saurari dukkan sassan ta ce kuma zata gabatar da hukumcinta ranar 19 ga watan Oktoba.

A ranar jumma’ar, Habre ya roki wannan kotu ta ECOWAS da ta umurci Senegal ta biya shi diyyar dala miliyan 11. Lauyan Habre, Francois Serre, yace idan har kotun ta yanke shawarar cewa an keta masa hakkin, to ya cancanci a biya shi diyya a saboda cin zarafin da ake masa a shari’ance.

Tsohon shugaban na Chadi, Hissene Habre, yana barin kotu a Dakar tare da ganduroba a 2005.
Tsohon shugaban na Chadi, Hissene Habre, yana barin kotu a Dakar tare da ganduroba a 2005.

Tsohon shugaban na Chadi ya gudu zuwa Senegal ya nemi mafakar siyasa a bayan da aka hambarar da shi a 1990. Ana zarginsa da cin zarafin bil Adama da kashe dubban abokan adawar siyasa a shekaru 8 da yayi kan mulki. Senegal ta fara yi masa daurin talala a cikin gidansa tun 2000. A 2006, Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta bukaci Senegal da ta gurfanar da Habre gaban shari’a da sunan Afirka. Tun lokacin, Senegal ta kafa dokokin da zasu ba ta ikon yin hakan.

Lauyoyin dake kare Habre sun ce Senegal ta kafa wadannan dokokin ne kawai domin hukumta shi, kuma babu ta yadda za a iya amfani da su domin hukumta laifuffukan da ake zargin an aikata tun kafin a kafa dokokin. Amma lauyoyin gwamnatin Senegal sun fadawa kotun ta ECOWAS a Abuja cewa karar da ya shigar gabanta ba ta da tushe.Wani lauyan gwamnatin Senegal mai suna Boubacar Cisse, yace su na sa ran kotun zata yi watsi da bukatun Habre. Yace Senegal ta sanya hannu kan yarjejeniyoyi na duniya kuma tana shigar da su cikin dokokinta.

Sadel Ndiaye shi ma lauya ne na gwamnatin Senegal, ya kuma ce Habre yayi riga malam zuwa Masallaci da wannan kara ta sa. Yace a wannan lokacin dai, Senegal ta kafa tsarin dokokin da zasu ba ta sukunin gurfanar da Habre a gaban shari’a ne amma ba ta gurfanar da shi ba. Ndiaye yace tun da ba a gurfanar da shi gaban shari’a ba, babu ta yadda zai ce an take masa hakki, kuma dokokin da Senegal ta kafa zai shafi kowa. Amma lauyoyin Habre sun musanta wannan, su na masu cewa ai tuni har Senegal ta fara shirye-shiryen gurfanar da shi gaban shari’a.

XS
SM
MD
LG