Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun kolin Amurka zata fara sauraron hujjoji kan kafa dokar inshora


Wadansu mutane a gaban kotun kolin Amurka

Yau litinin kotun kolin Amurka zata fara sauraron hujjoji daga lauyoyi kan garabawul ga dokar inshoran kiwon laifya

Yau litinin kotun kolin Amurka zata fara sauraron hujjoji daga lauyoyi kan garabawul ga dokar inshoran kiwon laifya, shekaru biyu bayanda shugaba Obama ya sanya hannu kan dokar da ta janyo rarrabuwar kawunan Amurkawa.

Kotun zata saurari kalubale ga dokar daga kwamishinonin shari’a na jihohi 26 wadanda suka dage cewa dokar ta sabawa tsarin mulki, da keta ‘yancin walwala ta wajen tilastawa kusan dukkan ‘yan kasa su sayi inshoran kiwon lafiya.

A cikin kwanaki uku alkalan kotun su tara, zasu saurari hujjoji na tsawon sa’o’I shida, wannan shine lokaci mafi tsawo da kotun ta kebe domin sauraron hujjoji, rabon da tayi haka tun a wajajen 1960.

Dokar wacce ake yiwa lakabi da “Obamacare” tana hankoron samarwa miliyoyin Amurkawa inshorar kiwon lafiya da ahalin yanzu basu dashi.

Dokar ta zama abin hadin kai tsakanin masu ra’ayin mazan jiya, wadanda suke cewa sauye-sauyen zasu mika batun kiwon lafiya hannun jami’an gwamnati maimakon likitoci, kuma hakan zai rusa ingancin shirin kiwon lafiya.

Babban abinda ake bukatar kotun ta tantance shine ko daya daga cikin ginshikin dokar na tilastawa Amurkawa sayen inshora yana kan hanya.

Masu adawa da wannan sharadi suna cewa majalisar dokokin Amurka bata da hurumin tilastawa Amurkawa sayen inshorar kiwon lafiya. Gwamnatin Obama ta tsaya kan bakanta cewa, majalisar dokokin Amurka tana da hurumin kafa wannan doka karkashin tsarin mulkin Amurka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG