Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotunan Kararrakin Zabe Na Jihohi Hudu Na Zama a Abuja


Kotu

Tabarbarewar tsaro a wasu jihohi hudu ya tilastawa kotunan sauraran kararrakin zabe cigaba da zama a birnin Abuja.

Kararrakin zaben gwamnoni da 'yan majalisu daga jihohi hudu na gudana a birnin Abuja saboda yanayin tsaro a jihohinsu.

Jihohin da suka fada cikin tabarbarewar tsaro sun hada da Adamawa da Borno da Rivers da Yobe.

Kodayaushe kotunan ke zama magoya bayan 'yan takaran na kwararawa zuwa Abuja saboda su saurari yadda ake gudanar da kararrakin.

Modibo Bakare wani lauya dake Abuja dake zuwa irin wadannan kararrakin yace da wuya a kawo kara rana daya da shaidu kana a yanke hukumci duk a rana daya. Yawancin lokaci idan an gabatar da kara sai alkali ya sa ranar da zai fara sauraro.

Duk wadanda karar ta shafa zasu koma su yi shiri. Mai gabatar da kara zai shirya ya kawo shaidu. Haka ma wanda ake tuhuma lauyan dake kareshi shi ma zai kawo shaidu.

Babu inda aka ce alkali ya yi hanzari ya yanke shari'a.

A karar da ta fito daga jihar Rivers gwamnan jihar Mr. Wike ya nemi kotun ta rushe kanta da kanta bisa zargin wai ba'a kafata kan ka'ida ba. Amma alkali Mu'azu Pindiga ya shure bukatar inda yace shugabar kotun daukaka kara ce ta kafa kotun bisa ga dokokin kasa.

Zaman kotunan a Abuja bisa ga dalilan tsaro bai kawar masu da huruminsu ba.

A kotun dake zama a Nyanya kan jihar Yobe ta kammala sauraren karar. Dan takarar PDP Adamu Maina Waziri shi ya kalubali zaben gwamna Ibrahim Geidam na APC. Maina Waziri ya bukaci a soke zaben gwamnan

Lauyoyin sashen masu kara wato Maina Waziri sun kammala gabatar da shaidu. Yanzu sashen kariya na Ibrahim Geidam ke gabatar da nasu shaidun.

Hassan Gimba na bangaren Adamu Maina Waziri ya nuna suna jin dadin yadda shari'ar ke gudana. A wani hannun kuma bangaren gwamna Ibrahim Geidam hankalinsu a kwance yake har ma suna cewa Adamu Maina Waziri Allah ya bashi baiwar faduwar zabe.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG