Accessibility links

Krista da Musulmai matasa sun yi taron neman zaman lafiya a Gombe


Musulmai na salla yayin da kristoci sun yi masu kariya

Hadakar kungiyoyin matasan Krista da na Musulmai sun yi taron neman zaman lafiya a Gombe

An shawarci matasan Krista da na Musulmai na jihohin arewa maso gabashin Najeriya kada su bari shugabannin addini ko na siyasa su yi anfani dasu wajen tada zaune tsaye a tsakanin al'umma. Wato kada su bari a yi anfani dasu a bata zamantakewar mutane.
An bada shawarar ne a taron hadakar kungiyoyin matasan Krista da na Musulmi na jihohin da aka yi a Gombe birnin Jihar Gomben Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya.

Sakataren hadakar kungiyoyin Krista Adamu Sambo ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kawunan matasa game da mahimmancin guje wa tashin hankali a jihohinsu. Ya ce kada su yarda da wani pasto ko limami da ya nemi su tayar da hankulan mutane. Ya ce ba zasu yarda da duk wanda ya nemi yin anfani da su ba domin aiwatar da ta'addanci.

An gargadi shugabannin addini da ma na siyasa kada su kuskura su kawo ma matasa rudani. Haka ma shugaban matasan Musulmai Mohammed Buhari ya bukaci matasan Musulmai da na Krista su hada kai su nemi zaman lafiya. Ya ce su yi watsi da duk wata shawara da ta nemi haddasa tashin hankali tsakaninsu.

Ga karin bayani a rahoton da Abdulwahab Mohammed ya shirya.

XS
SM
MD
LG