Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gyare-Gyare A Sabon Dandalin Sashen Hausa Na Muryar Amurka


Gyare-Gyare A Sabon Dandalin Sashen Hausa Na Muryar Amurka

Muna ci gaba da kokarin inganta wannan dandali da sabbin bayanai, da kuma magance matsalolin da ka taso domin ku masu sauraronmu.

Masu sauraronmu da yawa sun rubuto su na kukar ko a yanzu ba su iya kama shirye-shiryenmu kai tsaye lokacin da ake watsawa, ko kuma dai ba su iya aiko mana da sako ta hanyar cika fom din dake karkashin Hanyar Tuntubarmu. To a gafarce mu.

Watakila ya zuwa lokacin da kuke karanta wannan, kun fara iya cika fom din dake wannan dandali kuna aiko mana da shawarwari da ra'ayoyinku. Mun ji kukar da ku ka yi kan wannan, mun kuma gano matsalar, har an kaddamar da kokarin gyara ta.

A yanzu kuna iya sauraronmu kai tsaye lokacin da muke watso shirye-shirye ta hanyar matsa shirin da ake bukata, na Safe ko na Hantsi ko Rana ko Dare a daidai lokacin da aka fara watsa shirye-shirye.

Ga wadanda ba su ga ra'ayoyinsu kan labaran da muka buga ba, wannan ma mu na nazarinsa, kuma zamu gyara wannan matsala nan gaba kadan.

Muna marhabin da shawarwari da irin ra'ayoyin da kuke aiko mana a koyaushe, muna kuma fatar za ku ci gaba da yin hakan. A kuma ci gaba da sauraronmu. Allah Ya bar zumunci.

XS
SM
MD
LG