Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kumbon Phoenix Ya daina Aiko Da Sako Daga Kan Doron Duniyar Mars


Hoton Duniyar Mars
Hoton Duniyar Mars

Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta ce kumbon Phoenix a yanzu ba ya iya aiko da wani sako daga kan jar kasa ta duniyar Mars.

Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta ce kumbon nan mai suna Phoenix dake kan doron duniyar Mars a yanzu ya daina aiko da wani sako daga duniyar mai jar kasa.

Masana kimiyya a sashen bincike da kera kumbuna na hukumar NASA dake Pasadena a Jihar California, sun ce a yanzu sun tsinke tsammanin jin wani abu daga kumbon na Phoenix a bayan da wani kumbo mai suna Mars Odyssey dake zagaya duniyar ta Mars ya bi ta saman inda kumbon Phoenix har fiye da sau dari biyu, amma ya kasa tuntubarsa ta wayar iska.

Kumbon Phoenix a kan duniyar Mars, kyamararsa tana kallon kasa.
Kumbon Phoenix a kan duniyar Mars, kyamararsa tana kallon kasa.

Kumbon Phoenix mai samun lantarkinsa daga hasken rana, ya sauka a kusa da kuryar arewacin duniyar ta Mars a ranar 25 ga watan Mayun 2088, ya kuma fara tattarawa, da bincike tare da aiko da sakamakon bincikensa kan irin kasar duniyar. Daga cikin abubuwan da kumbon Phoenix ya gano, har da kasancewar wani sinadari mai suna Perchlorate mai sanya wasu abubuwa su na yin tsatsa. Ana samun wannan sinadari, wanda ke kashe wasu halittu ya raya wasu, a nan duniyar bil Adama.

Kumbon ya shafe watanni biyar yana aiko da sakonnin sakamakon bincikensa, watau watanni biyu fiye da lokacin da aka yi tsammanin zai yi aiki. Da ma dai masana kimiyya na Hukumar NASA ba su yi tsammanin kumbon na Phoenix zai iya jurewa hunturu mai tsanani a duniyar ta Mars ba.

Hotunan dabam da wani kumbon na Amurka mai suna "Mars Reconnaissance Orbiter" mai kewaya duniyar Mars ya dauka, na kumbon Phoenix, sun nuna alamun kankara ta lalata fallayen tattara hasken rana na kumbon Phoenix.

XS
SM
MD
LG