Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabab Tayi Barazanar Kawo Hari Amurka da Canada


Katafaren kantin dake Minnesota

Biyo bayan barazanar da kungiyar al-Shabab tayi an tsananta tsaro a duk katafarun kantunan Amurka

An tsananta matakan tsaro a manyan kantunan zamani biyu, daya a Amurka guda kuma a Canada, sakamkaon barazanar da mayakan sakan al-Shabab da suke Somalia suka yi.

Masu lura da katafaren kantunan da ake kira "Mall of America" dake jihar Minnesota a arewacin kasar, da kuma na Canada da ake kira Edmonton dake yankin Edmonton. Duk sun fidda sanarwa suna cewa sun kara matakan tsaro a wuraren, bayan da kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida ta fidda wani fefen vidiyo ranar Asabar, inda yi kira a kai hari kan irin wadan nan kantuna a kasashen da suke yammacin duniya.

Sanarwar ta al-Shabab ta ambaci wasu wuraren kasuwanci a Amurka, da Canada da Britaniya, ciki harda kantin dake Minnesota.

Kakakin fadar white House Josh Earnest ya fada jiya Litinin cewa babu wata shaida mai inganci danagne da wani shirin kai hari kan kantin dake Minnesota, duk da haka yace akwai bukatar Amurka ta kara maida hankali.

Da take magana kan barazanar, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, ta kira vidiyon na al-Shabab da cewa farfaganda ce kawai, ta kara da cewa hukumomin tsaron Amurka basu da wani bayani cewa wadansu suna shirin aiwatar da barazanar da al-Shabab tayi.

Ahalinda ake ciki kuma, wata kotu ta yankewa wasu mutane biyu 'yan jihar California daurin shekaru 25 a fursina saboda samunsu da laifin kulla makarkashiyar taimakawa 'yan ta'adda su kashe Amurkawa a kasashen waje.

XS
SM
MD
LG