Accessibility links

Kungiyar Al-Shaban Ta Fice Daga Garin Kismayo


Wani Sojan Kasar Kenya dake rukunin sojojin dake kai farmaki a Somalia.
Kungiyar mayakan al-Shabab ta kasar Somaliya tace ta janye daga wuri na karshe dake karkashin ikonta a kasar.

Kungiyar ta sanar yau asabar cewa, ta fice daga birnin Kismayo dake da tashar ruwa. Jiya jumma’a dakarun kasar Kenya suka kai a birnin a wani farmaki da aka kai da nufin kakkabe mayakan. Kungiyar alshabab taci alwashin maida martani.

Rundunar sojin kasar Kenya tace harin da aka kai jiya jumma’a ya kunshi mayakan kasa da na teku da kuma na sararin sama, an kuma kai harin ne tare da hadin kan Kungiyar Tarayyar Afirka da dakarun gwamnatin Somaliya.

Wadansu mazauna garin sun ce yau asabar mutane suka yi ta wawashe gine ginen da ma’aikatan kungiyar al-Shaban suka zauna.

Dakarun kasar Kenya sun yi ikirarin cewa, sun kwace ikon wadansu sassan arewacin birnin suna kuma shirin kutsawa kudancin a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
XS
SM
MD
LG