Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hausawan Kamaru Tayi Taro A Birnin Douala


Taron kungiyar Hausawan Kamaru a Douala

Hausawan Kamaru sun yi taro a Douala babban birnin kasuwancin kasar domin fadakar da juna akan mahimmancin kare al'adunsu tare da fadakar da juna akan zamantakewa da neman ilimin zamani da na addini

Sanadiyar rashin rungumar ilimin zamani wasu matasan Hausawan na Kamaru suna fadawa cikin abun da bai shafesu ba.

Shugaban kungiyar na kasa Musa Useni yace duk da cewa kakannin kakananinsu da suka kawosu sun kafasu kan tafarki mai kyau ta sanadiyar gina masallatai da makarantun addini da ma wasu amma yanzu sun lura cewa wadanda suka zama Hausawan Kamaru basu gina akan gurbin da aka yi masu ba.

Malam Musa Useni yace iyayensu na yanzu nada sakaci da yawa wajen sa yara makaranta da kuma sasu su koyi sana'o'i domin su ma yaran su zama jaruman gwarzaye ta yadda idan za'a yi siyasa a yi harkar da zata taimakawa hausawan Kamaru gaba daya.

Yanzu sun kuduri aniyar hadin kai akan neman ilimi dalili ke nan da shi shugaban ya tara su domin ya fadakar dasu akan tarihin hausawa saboda da yawa cikinsu basu san tarihinsu ba.

Mai martaba sarkin hausawan birnin Idea Alhaji Zakari Muhammadu ya yaba da yadda hausawan suka bullo daga kusurwowi hudu na kasar saboda wai suna samun matsaloli da yawa. Saboda haka ya kamata su yi nazari akan abubuwan dake kawo masu matsaloli a cikin harkokinsu da rayuwarsu.

Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG