Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS ta Hallaka Sojojin Tunisia Biyu


Firayim Ministan Tunisia Habib Essad

Rundunar sojojin kasar Tunisia sunce, ‘yan kungiyar ta’addar ISIS sun hallaka musu sojoji biyu masu binciken inda aka yi garkuwa da wasu jami’ansu a yammacin yankin kusa da kan iyaka Algeria.

Sannan kuma sojoji guda hudu sun sami rauni duk a lokacin neman a yankin tsaunin Sammana, kamar yadda kakakin sojojin Belhassen Oueslati ya bayyana.

Sojojin Tunisia dai na aiwatar da ayyukansu a yammacin Tunisia, wurin da jami’an tsaro da dama ke rasa rayukansu wajen yakar masu tsatsaurin ra’ayin ISIS.

Sojojin basu tantance ko wadanne ‘yan kungiyar ta’addancin suka kai harin ranar Litinin din ba.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai hare-hare guda biyu a shekarar nan da aka kai a wasu wuraren yawon bude idanu a kasar da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 59.

A makon da ya gabata kungiyoyin fararen hular Tunisia suka ci babbar lambar yabo ta Nobel, sakamakon yadda suka daidaita tsakanin masu tsatsaurin ra’ayin Islama da ‘yan majalisun adawa na kasar.

Sun kuma taimaka musu wajen fafutukar gina siyasar kasar. Juyin-juya halin kasashen Larabawar da ya yadu, ya faro ne daga Tunisa a shekarar 2010 zuwa 2011.

Kasar ta Tunisia ta sami nasarar ci gaba da aiwatar da siyasa, a yayin da kasashen Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakita ke fama da matsalar rashin daidaito.

XS
SM
MD
LG