Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Mata Na Gangamin Zaman Lafiya A Arewa


Mata

Cibiyar tattaunawa don wanzar da zaman lafiya da ake kira “Center For Humanitarian Dialogue” ta karfafa rungumar dabi’ar yafewa juna a yankunan da aka samu fitina a matsayin hanyar samun ci gaban al'u'mma a maimakon rike juna a zuciya da tunanin ramuwar gaiya.

Jami’an cibiyar sun gayyato kwararru a wani gagarumin taro a Abuja don cusa wannan dabi’a ga al’ummar arewa ta tsakiya da ta yi fama da fitinar makiyaya da manoma da kuma arewa maso gabashin kasar da ta yi fama da Boko Haram.

Gloria Thomas daya daga cikin shugabannin cibiyar ta bayyana cewa sun fara aikin fadakarwar ne tun 2014 kuma kawo yanzu zasu iya cewa, sun fara ganin tasirin aikin.

A cikin hirar ta da Sashen Hausa, wata wadda ta fuskanci tashin hankali da illar Boko Haram Hajiya Gana Sulaiman tace, wadanda suka sami kansu a irin wannan yanayin suna samun kalubalai da dama.

Mahalarta taron sun bayyana yadda yafewa juna ya taimaka wajen kwantar da hankalida maido da yarda da kyakkyawan zamanta kewa tsakanin al'ummar jihar Filato da fitinar bambancin addini da kabilanci ke addaba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

Taron mata kan zaman lafiya-2:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG