Accessibility links

Kungiyar Tarayyar Afrika ta kara wa'adin jagorancin Jean Ping


Shugabannin kasashen Afrika

Kungiyar tarayyar Afrika ta kara wa’adin jagorancin babban jami’inta Jean Ping bayanda yunkurin zaben magajinshi ya gamu da cikas.

Kungiyar tarayyar Afrika ta kara wa’adin jagorancin babban jami’inta Jean Ping bayanda yunkurin zaben magajinshi ya gamu da cikas.

Ping wanda shine shugaban hukumar Kungiyar hadin kan Afrika, mai kula da harkokin gudanarwa na kungiyar, bai sami isassun kuri’un da yake bukata na kada abokin hamayarshi shugaban Afrika ta Kudu domin wani wa’adin shugabanci na shekaru hudu ba, a zaben da aka gudanar jiya Litinin.

Shugaban kasar Benin Boni yayi wanda yake rikon shugabancin kungiyar da ake karba karba ya bayyana cewa, shugabannin kungiyar sun amince da kara wa’adin shugabancin Ping da sauran jami’an gudanarwa na hukumar zuwa watan Yuni, lokacin da kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrikan zasu yi taronsu na gaba.

An kushewa Ping wanda yake daga Gabon, a kan rawar da kungiyar Tarayyar Afrikan ta taka yayin tashin hankalin kasar Libya da kuma Ivory Coast, yayinda jami’an diplomasiya suka ce gaza lashe zaben wa’adin shugabanci na biyu alama ce ta nuna rashin gamsuwa da shugabancinshi.

XS
SM
MD
LG