Accessibility links

Kungiyoyin Agaji Na Kasa Da Kasa Sun Koka Kan Karancin Abinchi A Nijar


Wani mutum a gonarsa da fari yayiwa ba kyau.

Kungiyoyin bada agajin kasa da kasa sun koka da ganin yadda ake karancin kayan abinchi a jumhuriyar Nijer, haka kuma na yiwa al’ummar Nijer babbar barazana.

Kungiyoyin bada agajin kasa da kasa sun koka da ganin yadda ake karancin kayan abinchi a jumhuriyar Nijer, haka kuma na yiwa al’ummar Nijer babbar barazana. Kungiyoyin agajin sun yi kiyasin cewa ‘yan Nijer sama da miliyan shida ne yanzu ke fuskantar karancin abinchi.

Hadin gwiwar kungiyoyin agajin kasa da kasa, ciki harda hukumar raba kayan abinchi ta Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga kasa da kasa da su bada isassun kudi domin samar da isasshen abinchi tun daga yanzu kafin faduwar damuna, kuma ga dukkan alamu matsalar karancin ruwan sama, ta hada da kasashen Senegal da kuma Chadi, don haka suma ke fama da karancin abinchi.

Hadin gwiwar kungiyoyin agajin kasa da kasa sun yi kiyasin cewa za’a bukaci kudi sama da Dala miliyan metan da ashirin da tara domin samar da abinchi a jumhuriyar Nijer. Mai Magana ada yawun hadin gwira kungiyoyin agajin Gaelle Bausson tace sama da mutane miliyan uku ne a yanzu haka ke fuskantar yunwa a Jumhuriyar Nijer.

Bausson tana mai cewa matsalar tayi kamari har tasa ‘yan Nijer sun fara yin kaura, sun fara saida kadarorinsu, wasu matan ma har sun fara saida murjani da gwale-gwalen da suka adana don gaba, kai hatta dabbobinsu ma basu tsra ba domin wasu sun fara saida awakai da shanun da suke kiwatawa.Jami’ar tace babbar matsalar itace halin da kananan yara ke ciki domin akwai yaran da yawansu yah aura dubu talatin da suka daina zuwa makaranta. Don haka ya zama wajibi kasa da kasa su kaiwa jumhuriyar Nijer dauki.

Masana sun bada shawarar gaggauta daukan matakan inganta kasar noma da takin zamani a yankin sahel domin rage karfin gudun da Hamada keyi zuwa yankunan dake da kasar noma mai albarka a yankin Sahel.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG