Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama A Nijar Sun Lashi Takobin Ci Gaba Da Zanga-zanga


'Yan adawa dake kurkuku a Nijar

Kame kamen da mahukuntan Nijar ke yiwa masu zanga zangar kin amincewa da karin haraji bai hanasu shirya wani na gama gari ba da suka yi kira ga jama’a su fito ranar Lahadi mai zuwa su ci gaba da zanga zangar

Duk da kame masu zanga zanga da gwamnatin Nijar keyi, kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun lashi takobin ci gaba da yin zanga zanga akan kin amincewa da karin haraji cikin kasafin kudin kasar na wannan shekarar.

A cewarsu babu abun da zai katse masu hanzari bayan cafke masu adawa da dokar harajin 2018 a makonni biyu a jere bisa zargin wai suna gudanar da haramtaciyar zanga zanga a Birnin Yamai.

Kungiyoyin sun shirya wata sabuwar zanga zanga ta ruwan dare gama gari saboda zasu yita ne a duk jihohin kasar ba Yamai kadai ba ranar Lahadin dake tafe kamar yadda sanarwarsu ta tabbatar.

Gamaci Muhammadou daya daga cikin manyan shugabannin kungiyoyin ya bayyana jerin wuraren da zasu yi zanga zangar , da suka hada da Damagaran, da Agadez, da Diffa da dai sauran wuraren. Sun yi kira ga dukkkan ‘yan kasa su fito ranar Lahadi tun da sanyin safiya.

Ministan al’adu kuma kakakin gwamnatin kasar Asumanu Malam Isa a cewarsa a lokacin da kungiyoyin suka bukaci a basu izini su yi zanga zanga sun shaida masu cewa saboda dalilan tsaro ba za’a basu izini yin zanga zanga a Yamai ba. A Maradi da Zinder,shugabanin da suka shirya zanga zangar sun ruga kotu inda aka basu izinin su yi zanga zangar. Amman a Yamai da basu nemi izinin daga kotu ba, shi yasa gwamnati ta cafke saboda tamkar sun dauki doka a hannu ke nan.

Souley Barma na da karin bayani a rahotonsa

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG